Game Da Mu

Game Da Mu

HAUSA24 an Kirkireta ne a shekarar 2015, Hausa24 da ake yima lakani da ‘H24’ wasu Lokutan yana daya daga cikin shafukan Hausa na yanar Gizo dake saurin yaduwa gurin gabatar da shirye shiryen labarai irin na Siyasa da kuma Harkar finafinan Hausa wanda akafi sani da “Kannywood”, Nishadantarwa, Waazantarwa, Ilmantarwa, Fagen Kimiyyah da Fasaha, Na Nahiyar Africa baki daya.

Akowani Wata Shafin Hausa24 na samun dumbin mabiya shirye shiryen mu dare da rana cikin kowani yanayi saboda irin karuwar da kafar ke samar musu.

Babbar Manufar kirkirar wannan shafin shine domin bunkasa Yaren Hausa da samar da Labaran dake faruwa na nan cikin Kasar mu ta Nigeriya, nahiyar Africa da kuma Duniya baki daya, wanda hakan zai taimaka waje hada kawunan al’umma da al’adunsu da irin tsarin rayuwarsu.

Mafi akasarin masu sauraron shirye shiryen mu matasa da dattijai masu kimanin shekaru 15 zuwa 50  wadan sune kan gaba wajen habakar al’umma daga sassa daban daban na Nahiyar Africa, Turai da sauransu.

Meyasa Zaku Kasance Da Kafar Hausa24

Kafar Hausa24 zata tabbatar da kokarin ganin ta yada al’adu, dabi’u da daukacin yadda malam Bahaushe ke gudanar da rayuwarsa domin duniya ta dada fahimtar shin wai wanene Bahaushe.

Hausa24… Labarai a ko wani lokaci.