Abunda Yasa Aka Hana Sojin Nigeria Wallafa Hotuna A intanet

206
15
SHARE

Daga yanzu an hana sojojin Nigeria wallafa hotuna ko bidiyon ayyukansu a shafukan sada zumunta.

Wannan mataki dai ya biyo bayan fitar da wasu fayafayan bidiyo ne a kwanakin baya, inda aka nuna wasu sojoji suna korafin karancin abinci da sauran kayan aiki.

A wani jawabi da ya gabatar a madadin Shugaban rundunar sojin kasar Tukur Buratai a birnin Kaduna, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade ya yi kira ga sojojin da su yi taka-tsan-tsan.

Ya ce “Ina gargadin ku kan amfani da shafukan sada zumunta a lokacin da kuke cikin aiki.

Za ku iya jin kuna bukatar daukar hotunan abokan aikinku masu kyau, amma ku yi taka-tsan-tsan wurin yin hakan,” in ji shi.

Ya kara da cewa “ku kau cewa wallafa duk wani hoto ko bidiyo wanda ya shafi abokan aikinku ko kuma aikin naku kai tsaye”.

Ana dai yawan yada hotuna da bidiyon dakarun Nigeria musamman wadanda ke fagen dagar yaki da Boko Haram.

Me Ra’ayin ku akan hakan? Rubuta ta comment

 

 

15 COMMENTS

  1. gaskiya haka ya dace tawani wuri tawani wuri kuma yana da illa mai girma in suna hawaka shafukan sada zumunta zasu iya fadawa duniya damuwarsu

  2. Ya Zama Dole Suyi Amfani Da Shafikan Yada Zumunta Dan Ganin Samun Abun Da Ya Zama Wajibi Su Sameshi.In Har Hakan Zata Biya Bukatarsu Ta Dole.Kamar Ruwa,abinci Makaman Aiki,danme Za A Hanasu Yin Hakan.

LEAVE A REPLY